Allah Ya Yiwa Hassan Wayam Rasuwa

INNALILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJU’UN

Wasu rahotonni daga ƙaramar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna sun bayyana Allah ya yiwa shahararren mawakin hukumar nan, Hassan Wayam rasuwa.

Tun da farko ɗan marigayin ne Bello Hassan Wayam ya wallafa da sanarwar mahaifin na sa a shafinsa na fasebuk.

“Innalillahi Wai’nna Ilaihi Raji’un. Allah ya yi ma babana mai suna Hassan Wayam rasuwa yau Asabar. Ya Allah kai masa rahama, Allah kasa jinyar da ya yi ta zama kaffara a gareshi, ka sa dashi da mala’ikun rahama”

Ana sa ran nan gaba kaɗan za a yi jana’izarsa a gidansa da ke Layin Zomo, Falladan karamar Hukumar Sabon Gari a Jihar Kaduna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *