A Dawo Mana Da ‘Yan Sandan SARS Zamfara – Matawalle

Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Dokta Muhammad Bello Matawallen Maradun ya bayyana cewa su a Jihar Zamfara suna bukatar jami’an tsaron yan sandan SARS saboda irin aikin da suke gudanarwa a Jihar.

Gwamna Matawalle ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da manema labarai jim kadan bayan ya fito daga taron kungiyar Gwamnonin Arewacin Nijeriya da aka yi a Kaduna.

Matawalle ya ce su matsayinsu a Jihar Zamfara Shi ne suna bukatar jami’an tsaron yan Sandan SARS sakamakon irin kwazon aikinsu, don haka ya kara da cewa suna bukatar a zakulo su a duk inda suke a kawo masu su a Jihar Zamfara suna bukatarsu.

Kimanin makwanni biyu kenan da gwamnatin tarayya ta sanar da soke rundunar ‘yan Sandan SARS biyo bayan wata ƙazamar Zanga-Zanga da ta dake wakana a fadin ƙasar.

Sai dai a jawabin da shugaban kasa ya gabatar kai tsaye ga ‘yan Najeriya a ranar Alhamis ya bayyana haramta dukkanin wata Zanga-Zanga a ƙasar, biyo bayan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *