Muna Bin Kamfanoni Bashin Naira Biliyan N392 – Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ta ce tana bin kamfanonin gine-gine da ke kula da ayyukan hanyoyi 711 a duk fadin kasar nan har zuwa biliyan N392bn.
Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, ne ya bayyana hakan ranar Laraba a Abuja yayin zaman kare kasafin kudin a gaban kwamitin Majalisar Dattawa kan Ayyuka.
Ya ce bashin N392bn ya zarce na N276bn da aka gabatar don ayyukan hanyoyi a 2021.
Ya ce ya zama wajibi a daina ba da kwangilar sabbin ayyuka domin a kammala wadanda ake da su.
Ya ce ana bukatar naira tiriliyan 6.62tillion don daukar nauyin ayyukan hanyoyi 711 a duk fadin kasar, yana mai cewa rashin wadatar kayan aiki ya sanya fifiko yana da matukar muhimmanci.
Lokacin da shugaban kwamitin, Sanata Adamu Aliero ya ba da shawarar a yi amfani da kudaden da ke hannun hukumar fansho ta kasa don daukar nauyin wasu ayyukan hanyoyin, Fashola ya ce ba shi da ikon yin hakan.
Ya kuke kallon wannan Batu?