Ba Zamu Lamunci Duk Wani Yunkuri Na Hargitsa Najeriya Ba – Gwamnonin Arewa

Ƙungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya ta bayyana bacin ranta kan wasu bata gari da miyagun ‘yan siyasa da suka lashi takobin durkusar da kasar nan da kuma kokarin yin juyin mulki.

Gwamnonin sun yi mamakin ta wane dalili za’a cigaba da zanga-zanga bayan irin sauraro da biyayyar da gwamnatin tarayya da na jihohi suka yi.

A jawabin da aka saki bayan zaman gaggawan da sukayi a jihar Kaduna ranar Alhamis, gwamnonin sun yi kira ga ‘yan Najeriya su yi fito-na-fito da makiyan Najeriya ta hanyar goyawa shugaban kasa baya.

A cewar jawabin da shugaban kungiyar gwamnonin, Simon Lalong, ya sanyawa hannu, gwamnonin sun tattauna kan matsalolin tsaro da lalata dukiyoyin a sassa daban daban na kasar.

“Saboda damuwa kan abubuwan dake faruwa, gwamnonin Arewacin Najeriya sun hadu kuma sun tattauna kan lamarin,”.

“Kungiyar gwamnonin na jajintawa wadanda suka rasa rayukansu, wadanda suka jigata da wadanda sukayi asarar dukiyoyinsu.”


“Kungiyar na nuna bacin ranta kan wasu bata gari, masu amfani da addini, kuma ‘yan siyasa da suka lashi takobin durkusar da kasar ta hanyar neman juyin mulki.”


“Kungiyar ta yi kira ga ‘yan Najeriya su nuna rashin amincewarsu da wadannan makiyan kasar ta hanyar goyawa shugaban kasa baya.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *