Matasa Sun Kai Kari Tashar Talabijin Na TVC

An kai hari gidan Talabijin na TVC a Legas
Wasu da ake zargin ‘yan daba ne sun kai hari a gidan talabijin na TVC da ke Legas.

Wata ma’aikaciyar gidan talabijin ɗin ta wallafa a shafinta na Twitter cewa suna cikin gabatar da shiri kai tsaye dole suka katse sakamakon ‘yan daban da suka faɗo daƙin gabatar da shirye-shiryen na su.

A halin yanzu dai gidan talabijin na TVC ɗin ya ɗauke, ma’ana ba a nuna tashar.

Wani bidiyo da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta ya nuna yadda ake ƙona wasu daga cikin motoci mallakar gidan talabijin ɗin.

Rahotanni na nuna cewa gidan talabijin ɗin mallakar tsohon gwamnan Legas ne Bola Ahmed Tinubu, duk da cewa bai fito fili ya gasgata cewa shi ne ainahin mamallakin gidan talabijin ɗin ba.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *