#EndSARS: Na Gargaɗeka Da Kisan Masu Zanga-Zanga – Obasanjo Ga Buhari

Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya yi tir da amfani da karfi da sojoji su ka yi wajen tasa keyar masu zanga-zanga a Legas, lokacin da suke Zanga-Zangar Lumana.

Cif Olusegun Obasanjo ya ce gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ba ta dauki duk sauran matakan da ya kamata kafin ta kai ga baza sojoji ba.

Obasanjo ya yi wannan bayani ne a wani jawabi da ya fitar a game da murkushe masu zanga-zanga da jami’an tsaro ke yi, a cigaba da Zanga-Zangar EndSARS da ta shiga makwanni biyu a na yi a kudancin Najeriya.

Tsohon shugaban ya gargadi Buhari “a kan amfani da karfin soji da sauran jami’an tsaro wajen yi wa mutane karfa-karfa da nufin shawo kan rikicin.”

Obasanjo wanda ya mulki Najeriya tsakanin 1999 da 2007 ya ce tarihi ya nuna kashe masu zanga-zanga bai kawo kwanciyar hankali, sai ma akasinsa. Tsohon Janar din ya ce amfani da kan bindiga zai sa a gaza iya zama a kan tebur domin ayi sulhu.

Obasanjo ya yi kira ga shugaban kasan ya yi maza ya dauki mataki tun kafin abubuwa su yi kamari, a rasa yadda za ayi a fadin kasar.

“An yi ta’adi, amma za a iya shawo kan lamarin kafin ya rincabe gaba daya.” Inji Obasanjo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *