Kano: Za A Fara Hukunta Masu Batsa Wajen Tallan Magunguna

Gwamnatin jihar Kano ta kafa wani kwamitin aiki da zai kama duk wani mai sayar da maganin gargajiya da yake amfani da kalaman da ba su dace ba lokacin da yake tallar maganinsa.

Kwamitin wanda Kwamishinan lafiya na jihar Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa zai jagoranta, zai ƙunshi rundunar ƴan sandan jihar, KAROTA, HISBAH, da sauran hukumomin tsaro da jami’an kiwon lafiya, waɗanda za su kama tare da gurfanar da waɗanda aka samu da laifi a gaban kotu.

Babban Sakataren hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya masu zaman kansu ta jihar PHIMA, Dr Usman Tijjani Aliyu, ya sanar da haka lokacin da yake yi wa ƴan jarida bayani kan shirin kwamitin na fara aikinsa.

Dr Aliyu ya ce yin amfani da kalaman batsa lokacin tallar magungunan gargajiyar ya zama ruwan dare a cikin al’umma, kuma gwamnati ba za ta ido, ta bar hakan ya ci gaba ba.

A don haka ya yi kira gare su, da su zama masu bin hanyoyin da suka dace da addini da al’ada, wajen tallata magungunansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *