Mai Martaba Sarkin Zazzau Na 19 Mallam Ahmad Nuhu Bamalli Ya Ziyarci Masarautar Sokoto

A yau 20 ga watan Oktoba 2020, Mai Martaba Sarkin Zazzau Na 19, Mallam Ahmad Nuhu Bamalli a yau ya ziyarci masarautar Sokoto domin zuwa sanar da Mai Martaba Sarkin Sokoto sannan kuma Sarkin Muslim, Muhammadu Saad Abubakar na 20, nadin da aka masa kamar yadda al’ada ta bayyana.

Yana daya daga cikin al’adun Zazzau na kowane sabon Sarkin da aka nada na masarautar Zazzau ya kaiwa khalifan gaisuwa ta musamman sakamakon alakar dake tsakanin masarautun. A shekarar 1804 Mallam Musa, Sarkin Masarautar Zazzau na farko ya kasance daya daga cikin aminan Danfodio sannan an damka masa tutar khalifanci da yayi amfani da ita wajen kafa sansani a Zazzau domin yada addinin musulunci a fadin Arewacin Najeriya. Har wa yau kujerar Khalifanci da masarautar Zazzau sun ci gaba da wannan alakar dake tsakaninsu

Abun kulawa a nan shine Mai Martaba Sarkin Zazzau, Mallam Ahmad Nuhu Bamalli, yana da alakar asali daga Sultan Muhammad Bello (1817 zuwa 1837) wanda ya kasance daya daga cikin ‘ya’yan Shehu Uthman Dan Fodio sannan kuma shine Sarkin Musulm na 2. Saboda haka wannan ba ziyarar kawo gaisuwa bane kawai, ziyara ce wacce ta kasance na da ya kawo ziyara gida ga iyalansa.

Manyan mambobin masarautar Sokoto tare da al’ummar masarautar masu yiwa sabon Sarkin Zazzau alheri suka karbi bakuncin Mai Martaba Sarkin Zazzau na 19

Allah ja zamanin Sarki. Allah bashi nasara da mulki mai albaraka.

Allah ya ci gaba da kare shi #amin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *