Amurka Ta Yanke Shawarar Cire Sudan Daga Kasashen Da Ta Bayyana A Matsayin ‘Yan Ta’adda

Amurka ta yanke shawarar cire Sudan daga cikin jerin ƙasashen da ta ayyana a matsayin ƴan ta’adda.

Amurkan ta yi hakan ne a wani mataki na ban gishiri in baka manda, wato saboda Sudan din tayi alkawarin biyan diyyar fiye da dala miliyan dari uku ga Amurkawan da aka kashe a hare-haren ta’addanci.

Shugaba Trump na Amurka ne ya sanar da wannan mataki inda ya ce za a biya diyyar ne ga wadanda suka mutu a yayin harin da ke da alaka da na kungiyar al-Qaeda wanda suka kai kan ofisoshin jakadancin Amurkan da ke Kenya da kuma Tanzania.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *