Babu Ɗan Arewan Da Ya Taimaki Buhari Kamar Tinubu – Lado Suleja

Dan majalisar tarayya mai wakiltar Suleja, Gurara da Tafa dake jihar Neja, wato Honarabul Lado Suleja ya musanta zargin da wasu ‘yan Arewa ke yi na cewa tsohon gwamnan jihar Lagos kuma jigo a jam’iyyar APC, Sanata Bola Ahmed Tinubu yana da mugun nufi ga al’ummar Arewa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Honarabul Lado ya kara da cewa, Tinubu masoyi ne na hakika ga Shugaba Buhari da yankin Arewa da al’ummarta.

“Idan muka duba kaf mutanen yankin Kudu babu wanda ya bada gagarumar gudummawa a nasarar da Buhari ya samu wajen zama shugaban kasa. Domin ya yi amfani da kudinsa, hikimarsa ta siyasa da sauransu wajen ganin Buhari ya zama shugaban kasa”, cewar Honarabul Lado.

Honarabul Lado ya kara da cewa gudummawar da Tinubu ya baiwa Arewa da al’ummarta ko wasu manyan Arewar ma ba su bayar ba. Domin a cewar sa a lokacin da wasu manyan Arewa suka kwarewa Buhari baya, Tinubu da sauran yaransa na Kudu ne suka jawo Buhari a jiki domin mara masa baya wajen ganin ya zama shugaban kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *