Hukumar Sojin Nijeriya Za Ta kaddamar Da Shirin Murmushin Kada

Hukumar Sojin Nijeriya ta kammala dukkan shirye-shirye wajen soma shirin ta na shekara-shekara wanda ake kira CROCODILE SMILE a turance, wato MURMUSHIN KADA.

Hafsan Sojin Nigeria Laftanan Janar Tukur Yusuf Buratai ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya gudanar a babban sansanin soji dake Ngamdu a jihar Borno.

Buratai, wanda Shugaban sashen horar da jami’an Soji, Manjo Janar Nuhu Anbagzo ya wakilta, yace ana kaddamar da wannan shiri ne a wata ukun karshen shekara, kuma wannan shirin shine na 6 tun da hukumar sojin Nijeriya ta soma yin sa.

Tukur Buratai yace shirin wanda za’a soma shi daga ranar 20 ga watan October zai kammala ne 31 ga watan December.

“Wannan shirin ya kunshi dabarun aiki daban-daban kamar yaki da kutsen hanyoyin sadarwa da nufin bibiya da kuma zakulo masu yada farfaganda a kafafen sada zumunta na zamani”, inji Buratai.

Yace wannan shine karon farko da za’a yaki kutsen hanyoyin sadarwa a tarihin shirin Murmushin kada a dukkan hukumomin sojin Nahiyar Afrika.

A cewar Hafsan Sojin, shirin har ila yau zai kunshi aikin gano ‘Yan Boko Haram da suke kokarin gudu daga yankin Arewa Maso gabashin Nigeria zuwa wasu yankunan a sakamakon jin matsin yakar su da soji suke yi.

Daga karshe ya bada tabbaci ga ‘Yan Nijeriya masu kishin kasar cewa Hukumar Sojin Nijeriya, zata cigaba da tsaron dukiyoyi da rayukan al’uma, inda kuma ya kirayi ‘Yan Nijeriya da su goyi bayan hukumar, tare da fahimtar ta domin ta cimma nasara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *