EndSARS: Gwamnatin Tarayya ba za ta yarda da rikici a Najeriya ba – Lai Mohammed

Gwamnatin Tarayya ta yi gargadin cewa ba za ta bari a jefa kasar nan cikin halin ha’ula’i ba sakamakon tashin hankalin da ya dabaibaye zanga-zangar EndSARS.

Ministan Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana hakan a ranar Asabar lokacin da yake gabatar da wani shirin labarai na Gidan Talabijin a Najeriya mai taken “Fayil din karshen mako”.

Ministan ya ce wasu bata gari ne suka sace zanga-zangar da kuma mutanen da ke da wata manufa ta daban wanda yanzu haka su ke juya akalar Zanga-zangar.

Ya lura cewa wadanda suka fara zanga-zangar suna da manufa mai kyau, amma yanzu a bayyane yake cewa ba su da sauran ikon aiwatar da wani abu a cikin shirin su na farko sai iya abinda suka gani tunda yanzu ba sune ke juya Akalar ba.

“Zanga-zangar lumana wani bangare ne na dimokuradiyya kuma shi ya sa Gwamnatin Tarayya a cikin kwanaki 11 da suka gabata ta bi da masu zanga-zangar ta hanyar wayewa.

Amma, idan kuka kalli abin da ya faru da gwamnan jihar Osun, ya wuce batun zanga-zangar lumana ta adawa da wuce gona da iri da‘ yan sanda ke yi.

“Babu inda a duniya gwamnati za ta nade hannayenta ta kyale kasa ta fada cikin rikici.

“Yanzu haka ba mu da ma’amala da EndSARS sai dai wani yanayi mai rikitarwa da zai iya haifar da rashin tsaro idan gwamnati ba ta dauki wasu kwararan matakai don kare rayuka da rayuwar ‘yan Najeriya waɗanda basu ji ba ba su gani ba,” inji shi.

Ministan ya kara da cewa zanga-zangar ta wuce ta zaman lafiya domin an rasa rayuka kuma ‘yan Najeriya marasa laifi, ciki har da ma’aikata da dalibai, suna wucewa ta cikin mummunan yanayi.

Musamman, ya ce saboda masu zanga-zangar suna toshe hanyoyi da babbar hanyar ma’aikata wanda hakan na musu wuya su samu zuwa ofisoshinsu kuma su dawo gida yayin da yawancin ‘yan Najeriya suka makale a kan hanyoyin.

“Ba mu da wani abu game da zanga-zangar lumana amma akwai hanyoyin wayewa na yin hakan.

“Wannan shi ne ta hanyar zuwa wurin da ba za ka tayar da hankalin sauran ‘yan Najeriya ba saboda inda hakkinka ya tsaya, nan hakkin wasu ya fara,” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *