Annobar Jima’in Jinsi Daya (Homosexuality) A Cikin Al’umma

Wani abin haushi da takaici da ya bullo cikin al’umma a ‘yan shekarun 2000 din nan shi ne bala’in jima’in jinsi daya, wato ‘homosexuality’ a Turance. A iya binciken da na gudanar kusan duka manyan addinai na duniya sun haramta wanan mummunar dabi’ar, hadi da la’antar masu aikata ta. Duk da cewar a al’adance baza a rasa wata al’adar da ta yarda da hakan ba. Abin daure kai da mamaki shine; ko daddobi da basu da hankali ba a ganin suna aikata wannan mummunar dabi’ar, sai ga mutane da ubangiji ya azurta da hankali, ilimi da tunani suna aikata hakan.

Shin Menene Jima’in Jinsi Daya?

Wannan yana nufin namiji ya nemi dan uwansa namiji da sunan biyan bukata irin ta sha’awa ko kuma mace ta nemi ‘yar uwarta mace domin kawar mata da sha’awa da aka sani akwai tsakanin namiji da mace.

Bincike ya nuna wannan dabi’ar ta zama ruwan dare game duniya, a tsakanin maza da mata, yara kanana, matasa kai har ma da Dattijai. Ko me ke tunkuda mutane da afkawa wannan masifar? Wadannan dalilai da zan zayyano a kasa, suna daga cikin dalilai da bincike ya nuna suke saka mutane suna aikata wanan mummunar dabi’ar:

Talauci: A halin da duniya take ciki na rashi da matsi, da yawan mutane abinda za su ci ma yana gagarar su. Wasu masu arziki da ke irin wannan dabi’ar da abin duniya suke rudar mutane; mussaman yara kanana da Matasa har su afkawa wannan masifar domin a basu kudi su gudanar da rayuwarsu da su.

Rashin hakuri: Wasu yaran da sun fara tasawa hallayarsu ta sha’awa mai tsanani ke bayyana, kuma da yawansu suna karatu ne iyayensu na jira su kammala sannan su aurar da su. I dan suka kasa hakuri sai kaga sun fara neman hanyar rage wanan sha’awar; sai Shaidan yai ta kawata musu hanyoyin da za suke biyawa kansu bukata har su afka, tare da duban hakan zai fi musu rufin asiri tunda ba zancen daukar ciki ko yin sa.

Mu’amala da abokan banza:Idan mutum na mu’amala da mutanen banza, yau da gobe ko ba halinsu daya ba, wata rana za ka ga sun rinjayi mutum har sun saka shi a hanyar da suke.

Tabarbarewar tarbiya:A zamanin baya, iyaye sun fi kula da tarbiyar yaransu,ba kamar yanzu ba da mafi yawancin iyaye hankalinsu yafi karkata kan neman abin Duniya ba. Da yawa wasu yaran a gidajensu suke aikata irin wannan dabi’ar, wasu ma da ‘yan uwansu shakikai na jini ne, kuma a ce iyayensu basu gano ba su na aikata hakan ba a tsakaninsu. A zamanin mu ko tafiya iyayen mu suka ga mun canja sai sun bincike mu, balle har su gan mu da abinda basu suka siya mana ba.

Wayar hannu:Fasahar wayar hannu da kuma yanar gizo-gizo ta kawo shafukan sada zumunta na (social media), in da wasu ta nan suke samun wadanda za su rude su har su koyi wannan dabi’ar. Wasu ma daga kallon bideos na irin wannan masifar ta yanar gizo-gizon kawai sai Shaidan ya kawata musu su ji suna sha’awar fara aikata hakan.

Chamfi:An riga an chamfa cewar duk masu irin wannan dabi’ar arziki suke yi, hakan ke saka mutane da yawa afkawa cikin wanan dabi’ar. Wani lokacin ma Malaman tsubbu da bokaye ke ce wa, mutane bukatarsu baza ta biya ba sai sun aikata wannan dabi’ar, kuma saboda Shaidan ya riga ya musu huduba, sai su aikata saboda neman abin duniya.

Jahilci:Mafi yawan mutane jahilci ya musu katutu a rayuwarsu; shi ya sa za a ga suna aikata dabi’ar da ko daddobi ba a ga suna aikatawa ba. Kamar yanda na fada a sama kadan baya, dukkan addinai sun yi hani da wannan dabi’ar, duk mai hankali, sanin kansa, ilimi da kuma aiki da shi kuwa ba zai yi sha’awar aikatawa hakan ba.

Jaraba:Wasu kuma jarabawa ce kawai, kamar yanda ake samun masu jima’I da dabbobi. Irin wadannan mutanen abun kamar ciwo ne a jikinsu na aikata abinda hankali da tunani ma ba zai dauka ba. Kuma a duk lokacin da ya motsa musu sai sun aikata.

Menene Mafita?

Mafita daya ce; iyaye su tashi tsaye su saka ido ga tarbiyar yaransu, su san irin abokan da suke mu’amala da, kuma su dinga bibiyar abinda suke a social media da wayoyin su. Sannan mutane su sani, arziki da rashi duk na Allah ne, yana ba wa wanda ya so ya hana wanda yaki; ba don baya son su ba, sai dan ya jaraba imanin su, idan mutum ya yi hakuri a gaba sai ya samu abinda bai za ta ba. A takaice wani baya arzirta wani, kuma sabawa Allah ba shi zai saka ya baka abinda ka ke so ba, sai dai ka halaka kan ka. Daga karshe, Malaman addini su kara kaimi wurin yunkurar da al’umma azabar da Ubangiji ya tanadarwa masu aikata wannan dabi’ar. Hukuma kuma ta kafa doka mai tsanani da za ta hukunta wadanda aka samu da aikatawa. Ubangiji ka ji kanmu ka kare mu da zuri’armu daga aikata wanan mummunar dabi’ar!

Daga Sameerah Bello Shinko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *