Masu Yada Cewa Na Fice Daga Kwankwasiyya Karya Su Ke – Abba Gida-gida

A yau Juma’a wasu Jaridun Yanar Gizo sun Wayi gari suna ta yayata cewa wai na Fice Daga Kwankwasiyya Saboda zaɓen 2023, ina So Jama’a su sani wannan Labarin ƙarya ne ƙirƙirar sa aka yi.

Tsohon ɗan takaran gwamnan jihar Kano a jam’iyar PDP a zaben 2019, Abba Kabir Yusuf ya Bayyana haka a ta bakin wani mukusancin sa kuma na hannun Dama, Inda ya ƙara da cewa Labarin bai da tushe balle makama.

Majiyar Dimokuraɗiyya ta gano cewa a na Wannan Raɗe-raɗin ne Jim kaɗan da Shigowar AB Baffa Bichi wanda zuwa yanzu bai wuce kwanaki 40 da shigowar sa ɗarikar ta kwankwasiyya ba.

Kazalika ma Abba Kabir Yusuf ɗin ne ya riƙo hannayen sa zuwa ga shehin na Kwankwasiyya, Inji Rahoton.

Me zaku ce?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *