Ina samun CV na Mutane sama da 200 duk lokacinda na ziyarci wata Jaha – Inji Minista Pantami

Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki Dr Isa Ali Pantami ya bayyana cewa dole sai matasa sun tsunduma ga Sana’o’i fiye da jiran aikin Gwamnati.

A cewarshi, yan Najeriya sun fi maida hankali akan samun Takardar shedar karatu fiye da koyon dabarun Sana’o’i, inda ya kara dacewa akwai ayyuka da dama a fadin Kasar nan, amma rashin sanin Dabarun sarrafawa ya sanya an kasa yin wani abu.

Yace ” a wasu lokutta idan kaje kaddamar da aiki, duk wanda ka tarar zai baka Takardun neman aiki masu yawa domin ka nemar ma mutane aiki. Akwai lokacinda na ziyarci wata Jaha saida na dawo da CV na mutane sama da 200; wannan wani karamin misali ne daya kamata muyi tunani akan haka.

Wannan shine dalilan daya sanya kasashen da suka cigaba suka bullo da dabarun sana’o’i kala-kala, wanda hakan ya sanya yan Kasar su basa sha’awar aikin Gwamnati sai dai don sadaukarwa.

Pantami ya bayyana haka a ranar Juma’ar nan a lokacinda yake kaddamar da wani katafaren cibiyar Sadarwa ta zamani a Jami’ar Jahar Gombe wanda Hukumar bunkasa Harkokin Sadarwa ta Kasa ta gina wato-NITDA.

Yace a halin yanzu yana bakin kokari na ganin ya shigo da Abokanan aikin sa na sashen Zartarwa na Kasa domin Tabbatar da cewa an baiwa Dabarun Sana’o’i fifiko bayan Karatu da akayi a Makaranta.

Daga Usman Salisu Gurbin Mikiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *