Abubuwa 3 Da Ake Fama Dasu A Gidajen Aure A Yau

Wadannan abubuwan guda 3 da zan jero sune tushen duk wata matsala da muke fama da ita a gidajen aure a yau. Na kawo su ne a takaice, zan Kuma dauke su daya bayan daya nayi bayaninsu sosai da yadda zamu dauki matakin gyara inshaa Allah.

1- Rashin tsoron Allah: Zan fara ne da tsoron Allah saboda shine mabudin dukkan aikin alkhaeri, kuma makullin dukkan sabo da son zuciya. A gaskiya yanzu akwai karancin tsoron Allah a cikin al’umman mu, khasatan a zamantakewan aure. Idan nace rashin tsoron ba ina nufin rashin ilimi ne ba ko rashi sanin ya kamata, a’a an sani ake take sanin a biyewa so zuciya. Mafi yawan matsalolin aure a yau suna samuwa ne daga bin son zuciya da yin abinda aka ga dama sabanin abinda Allah yayi umurni. Da dukkan mu mazan da matan za mu ji tsoron Allah muyi biyayya ga tsarin Allah da wallahi matsalolin da muke fama da su da yawa sun yi kaura.

2- Rashin sanin muhimmancin aure: Aure shine hanya guda daya tilo ta samar da nagartacciya kuma sahihiyar al’umma, sannan kuma shine kadai hanyar gina kowace irin alaka. Amma Maganar gaskiya shine hausawa yanzu da yawa ba mu san muhimmancin aure ba, kawai dai muna fada ne a baki, sbd mun bar abin da yake da muhimmanci mun koma muna rara gefe. Abinda muka fi dauka da muhimmanci a sha’anin aure shine hidiman auren da sharholiyar da ake yi yanzu wajen biki. iyayen amarya hankoron su me zasu kai ma diyar su ta wuce gori, furnitures da sauran tarkacen da idan suka yi wasa za’a dawo masu dasu tare da diyarsu, dalili kuwa taje tana ma miji abinda ta ga dama saboda rashin sanin muhimmancin mijin da auren gaba daya. Ango da Amarya kuma sun fi maida hankalin su wajen tsara ebents din bikin su yanda zasu shiga tsara.

Shi zaman auren a kashin kan shi bamu dauke shi da wani muhimmancin da za’a shirya masa ba, mun dauke shi wani abu na je ka nayi ka, ko wani al’ada da aka saba da shi. Mun manta cewa addini ne, kuma ibada ne me girman gaske da yake kunshe da falala me tarin yawa, kuma kamar sauran ibadodi shi ma aure Allah (T) ya tsara mana yanda zai kasance, tun daga neman auren har zaman gidan auren, akwai abubuwa masu muhimmancin gaske da ya kunsa. Amma ba sune a gaban mu ba, shiyasa aure yanzu ya zama abinda ya zama, to mun bar umurnin Allah a cikin sa, mun wawaitar da shi, ta ya zamu ga yanda muke so?

3- Rashin ilimin zaman aure: Bayan rashin sanin muhimmancin auren sai kuma rashin sanin ilimin auren, wanda Ilimi ne me girma da fadin gaske da ya kamata kowane saurayi da budurwa su samu kafin su yi aure. Iyaye na taka muhimmiyar rawa a wannan bangaren musamman iyaye mata, saboda mafi rinjayen tarbiyyan yaranku mazan da matan duk yana hannunku ne. kenan ku kuke da alhakin koya musu zamantakewa, da yanda zasu gina gidajen da sune zasu jagoranta a gaba. Kuma hakan ba zai yiwu ba har sai ku ma kun siffantu da sifa me kyau a zamantakewan ku, irin siffan da kuke so ku dora yaran ku akai, domin shi yaro yana da kula, abinda ake aikatawa yake gani yafi yi mishi tasiri akan abinda ake fada masa. Ku tarbiyyantar da yaranku cikin so, kauna da tausasawa, ku koya ma yaranku maza yanda zasu zama mazajen wasu, kuma iyayen wasu, yaranku mata su san kan su, su iya kula da kan su a matsayin su na mata, su san hakkokinsu, su san hakkokin mazajen su a kan su, su san yanda zasu fahimci mazajen su, su zauna da miji cikin girmamawa da kyautatawa, su san ya zasu tarbiyyantar da yaran da zasu haifa a gaba. Amma yanzu yarinya duk ba zata san wadannan daga wajen mahaifiyar ta ba, illa iyaka za a koya mata girki da gyaran gida ne, sai social media ne da kawaye suke kazagin zakal akan wannan, wanda bai kawo mana wani mafita sai ma rudani, saboda kowa da inda alkalamin sa ya dosa, kowa ya kan rubuta son ran sa ne ya yada. Wannan kalubale ne gare ku Iyaye ku tashi tsaye ku dauki ragamar sanar da yaranku Ilimin zamantakewan aure, menene aure, menene a cikin shi, matsalolin shi da kuma hanyar gyara ko kuma ku bar social media da kawaye su bude idon yaranku su raba masu hankali.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *