Zaben 2023: 18 Ga Watan Fabrairu Za A Gudanar Da Zaben Shugaban Kasan Najeriya – INEC

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta fitar da sanarwar cewar zata gudanar da zabukan Shugaban kasa a ranar 18, ga watan Fabarerun shekarar 2023, dake tafe.

Shugaban hukumar zaben mai zaman kanta (INEC) Farfesa Mahmood Yakubu, ne ya bayyanawa Yan majalisun wakilan tarayya yau Talata a babban birnin tarayya Abuja.

Farfesa ya ce daga yau Alhamis saura kwanaki a kalla 855, suka rage a gudanar da zaben Shugaban kasa a kasar mu Najeriya kamar yadda ya bayyana.

Kawo yanzu a Najeriya babu wani Dan takara daga Jam’iyyun adawa dana mulki daya fito gadan-gadan ya bayyana aniyar sa ta tsayawa takarar shugabancin kasar nan, sai dai jiga-jigan Yan siyasa sun fara harin karbar kujerar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *