Mai Martaba Sarkin Zazzau Alh. Ahmed Nuhu Bamalli Ya Ziyarci El-Rufai, Ya Lashi Takobin Yin Aiki Da Gwamnatin Jahar Kaduna

A ranar Laraba 14 ga watan Oktoba 2020 mako daya cak da hawa karagar mulki Mai Martaba Sarkin Zazzau na 19, Alhaji (Amb) Ahmed Nuhu Bamalli, ya ziyarci mai girma gwamnan jahar, Malam Nasir El-Rufai, a fadar Gwamnatin jahar Kaduna Kashim Shettima House domin kaiwa gwamnan gaisuwa na musamman.

Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji (Amb) Ahmed Nuhu Bamalli, ya bayyanawa gwamnan jahar cewa yana nan yana shirye-shirye a kan kudirinsa na wanzar da zaman lafiya, da samar da hadin kan al’umma, da isashen tsaro tare da samar da ci ga ga masarautar Zazzau inda ya kara da cewa zai hada kansa da kungiyar masarautun jahar Kaduna domin ganin an cimma wannan gurin domin samar da ci gaban jahar ga baki daya tare da aiki da Gwamnatin jahar wajen cimma gurin ta da samar da ci gaba da al’ummar jahar ga baki daya.

A yayin da ya ke jawabinsa Mai Martaba Sarkin Zazzau na 19, Alhaji (Amb) Ahmed Nuhu Bamalli, ya yi magana a kan muhimmancin hadin kan al’umma musamman ma ga sauran daulolin dake da gadon sarautar Zazzau inda ya ce kofarsa a bude take wajen yin aiki da kowa domin ci gaban al’umma. Ya ce babu shakka gurin kowane Yarima ne ya zama Sarki a duk lokacin da ake bukatar nada sabon Sarki amma karshen mutum daya (1) za a zaba idan wannan lokacin ya zo. Sarkin ya bayyana cewa yana da gadon sarautar Zazzau daga bangaren gidan sarautar Beri-Beri sannan kuma ya kasance suruki daga bangaren gidan sarautar Katsinawa domin shi ke auren daya daga cikin yaran marigayi tsohon Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris. Mai Martaba Sarkin Zazzau ya samu rakiyar wakilai daga kowane daular sarautar Zazzau wadanda suka hada da Katsinawa, da Beri-Beri, da Mallawa da kuma Sullupawa wadanda suke mulki a halin yanzu.

A na shi bangaren kuma mai girma gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya yi kira ga Sabon Sarkin da ya daura ci gaba daga inda marigayi tsohon Sarkin ya tsaya na kyauwawan aiyuka domin samarwa al’umma masarautarsa ci gaba. Gwamnan ya jaddada cewa da ilimi da wayewar Sabon Sarkin ba shi da wani fargaba a kan Sarki domin babu shakka masarautar Zazzau zata canza a karkashin mulkinsa sannan kuma ya ji dadin bayanin da Sabon Sarkin yayi game da kudirorinsa na samarwa masarautar Zazzau ci gaba. Inda ya ce yana sa ran a cikin kudirorin nasa akwai shirin ginawa mambobin masarautar sabbin gine-gine domin su ji dadin aiwatar da ayyukansu yadda kamata da hukumar kananan hukumomin dake karkashin masarautar Zazzau. A nan ne gwamnan ya furta cewa a na shi kokarin ya bada umurnin sauye fasalin tsohuwar fadar masarautar Zazzau domin ginawa Sarkin da majalisar masarautar gida da fadar zamani.

Gwamnan ya bayanin cewa an zabe Sabon Sarkin ne a lokacin da jahar ke fuskantar barazanar rashin isashen tsaro, da rashin aikin yi ga matasa, da barazanar shaye-shayen miyagun kwayoyi, tare da rashin jituwa a tsakanin alummar jahar. Inda ya ke kyauta zaton Sabon Sarkin zai yi amfani da kujerarsa wajen kawar da wadannan matsalolin da jahar ke fuskanta.

A yayin da gwamnan ke jiran bayanai kudirorin Sabon Sarkin gwamnan ya baiwa Sabon Sarkin tabbacin ci gaba da marawa mulkin Sabon Sarkin baya dari-bisa-dari sannan kuma ya masa al’adu’an Allah ya ja zamanin mulkinsa a cikin sa’a.

Mai Martaba Sarkin Zazzau na 19, Alhaji (Amb) Ahmed Nuhu Bamalli, ya kasance a birnin Kaduna tare da majalisar masarautar, da mataimakansa da kuma dogarensa. Ranar da Mai Martaba ya kaiwa gwamna ziyara rana ce wanda za a dade ana bada labarinta domin wadanda suka yiwa Sarki rakiya sun fito sanye da kayayyakin al’adun gargajiyar Zazzau gwanin ban sha’awa sannan kuma mutane da dama ma’aikatan gidan Gwamnatin jahar Kaduna sun fito domin mika gaisuwansu ga sabon Sarkin. Sarkin ya sake yiwa Ubangiji Allah godiya sannan ya kwanta da misalin karfe 12:00 na dare, da safiyar Allah misalin karfe 7:00 na safe gidan Sarkin ya sake cika da al’umma bayanin Allah wadanda suka kawowa Sabon Sarkin gaisuwa. Sarkin ya ci gaba da yiwa Allah godiya da ya ba shi mulkin masarautar Zazzau sannan kuma ya roki Ubangiji ya kare shi sannan kuma ya taya shi riko wajen tafiyar da mulkinsa. Bayan hakan Sabon Sarkin ya dauka hotuna sannan a nan take ba tare da bata lokaci ba ya koma Zaria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *