Ma’aikatan Hukumar Jiragen Sama Sun shiga yajin aiki na Gargadi

Ma’aikatan hukumar kula da filayen jiragen saman Najeriya FAAN, sun tsunduma yajin aikin gargaɗi na kwana guda a ranar Alhamis din nan, inda suke buƙatar gwamnatin ƙasar ta biya su dukkanin hakƙoƙinsu da su ke bi.

Ƙungiyoyin ƙwadago na hukumar sun kulle ƙofofin shiga babbar shelkwatar ta FAAN, inda kuma suka hana Ministan sufurin sama, Sanata Hadi Sirika yin wani taro da aka shirya wanda za a yi a ma’aikatar.

Dama dai, a yau ne ake sa ran ministan zai gana da shugabannin ƙungiyar ƙwadagon na FAAN to sai dai hakan ya ci tura sakamakon garƙame duk ƙofofin hukumar da ƙungiyoyin su kayi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *