Jinsin Fulani Sullubawa

Duk da yake mafi rinjayen masana tarihin Fulani sun bayyana cewa Fulani k’abila d’aya ce, daga tushe d’aya da suka shigo Afirka ta Yamma, wato k’etaren K’asashen Larabawa daga wajan K’asar Masar, daidai gab’ar Tekun Nilu zuwa K’asashen Sanagal da Libiya da Laberiya da Moroko da Aljeriya da Mali da Burkina-faso da Najeriya.

Sullub’awa kuma ana hasashen sun fito daga Sisillo ne, wanda ya auri Cippowo, ‘Yar Uwar Uthman Toroddo, wanda shi ne salsalar Mujaddadi Shehu Usman Danfodio tagammadahullah birahamatihi.

Saboda haka ma ne ake ganin Sullub’awa a matsayin abokan wasan Torankawa ( Zuriyar su Mujaddadi Shehu Usman Danfodio). Sullub’awa suna da surki da Wangarawa , suna kuma da had’i da Madingo da Madinka.

An ce sun fara magana da wani harshe da ake kira Wakore, kafin daga baya Harshen Fulatanci ya had’iye wannan harshe nasu( Wakore).

Sullub’awa suna cikin al’ummar da ke amfani da harshen Fulatanci na farko-farko da suka baro Futa -Toro ya zuwa K’asar Hausa.

A zuwa tsakiyar K’arni na 12, sun kafa Daular su a wani wuri da ake kira Zandam, da Sarkin su da ake kira Sarkin Sullub’awa.

Daga nan ne suka warwatsu ya zuwa sassa daban daban na K’asar Hausa dake zagaye da Kogin Rima na Sakkwato , ya zuwa Zazzau da wasu sassa na K’asar Katsina da Kano.

Sullub’awa a Karkashin Jagorancin Malam Ibrahim Dabo sun samu sukunin kafa gidan Sarauta a Daular Fulani ta Kano.
A shekarar 1819, Malam Ibrahim Dabo ya zamo Sarkin Kano na biyu a Daular Fulani, ya yi mulki har zuwa rasuwarshi a Shekarar 1846, daga lokacin ya zuwa yau , Zuriyar shi ke mulkin Kano. A Daular Fulani ta Zazzau, Sullub’awa sun samu kafa tarihi da samar da gidan Sarauta, domin Malam Abdulsalami ya zamo Sarkin Zazzau na 7 a Daular Fulani, a Shekarar 1853 har zuwa rasuwar shi a Shekarar 1857. Duk da yake daga gare shi Sullub’awa ba su sake samar da Sarki a Masarautar Zazzau ba ya zuwa yau.

A Katsina , Sullub’awa ta hannun Muhammadu Dikko sun kafa tarihin samar da gidan Sarauta domin kuwa an nad’a shi Sarkin Katsina na 8 a Daular Fulani ta Katsina , a Shekarar 1906.

Ya zuwa yau, Zuriyar sa ce ke mulki a Masarautar Katsina. Malam Jamo, k’ane ga Sarkin Kano Malam Ibrahim Dabo ya zauni K’iru . A Shuni da Rikina da Wamakko da Dingyadi da Sanyinna dake Masarautar Sakkwato, Sullub’awa ne ke mulkin su, wasu tun gabanin Jihadin Mujaddadi Shehu Usman Danfodio tagammadahullah birahamatihi.

Littafan da suka taimaka wajen wannan bincike sune:- 1. Ibrahim Ado-Kurawa 2019 Sullubawan Dabo: An Illustrated History 1819-2019. 2. Abdullahi Nasidi Umaru Waziri(Galadiman Daji) 2008 Daular Fulani a Kano 1806 -2002. 3. Usman Dalhat, Musa Hassan 2000: Alhaji Shehu Idris CFR , The 18th Fulani Emir of Zazzau. 4. Labo Yari 2007: Muhamman Dikko, Emir of Katsina and His Times 1865-1944. 5. Infakul Maisur na Sarkin Musulmi Muhammadu Bello.

Ibarahim Muhammad (Danmadamin Birnin Magaji) , Oktoba, 2020.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *