‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 15 A Katsina

Mutane 15 Mahara suka kashe a kauyen Dan Aji dake karamar hukumar faskari ta Jahar Katsina, a wani sabon harin da suka kai jiya Talata

Haka zalika Harin yayi Sanadiyyar raunata mutane da dama a yankin.

Wani mutum wanda ya tsallake rijiya da baya yace yaji maharan na Shan alwashin kora dukkanin Al’ummomin dake garuruwan ya zuwa garin Funtua.

Idan dai ba’a manta ba ko a irin wannan harin da suka kai a garin kadisau sun sha irin wannan alwashin.

Sai dai a yan kwanakin nan Sojoji na kai dauki, inda suke fatattakar su a duk lokacin da aka samu hari a wasu yankunan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *