Yadda Ake Hada Mulmulallen Kwallon Kifi (Fish Balls)

Kayan Hadi:

  1. Kifin sanyi, da kwai
  2. Tattasai, tarugu, albasa
  3. Curry, thyme, citta, tafarnuwa, kanunfari da
    Maggi, Gishiri, Man Gyada.

Yadda Ake Hadawa;


Ki sami ice fish masu kyau, sai ka wanke tafasa, bayan ya tafasu sai a sauke a barshi ya huce, sai a cire dukkanin tsokar a kwano. Sai ki farfasa shi shi sosai.

Sannan a daka tattasai, tarugu, da tafarnuwa su daku sosai. Sai ki zuba a kan kifin, sai ki dauko ragowar albasan ki yanka shi ‘kanana a kan kifin, kisa citta kadan, kisa curry, gishiri, thyme, dama sauran su.

Sai ki jujjuya su hade, daga nan sai ki rinka dunkula su kamar yadda hoton ya nuna, sai ki sami kwai ki kada a kwano, kisa maggi kadan da gishiri, sai kisa mai a wuta yayi zafi. Sai ki rinka dauko dunkulallen kifin nan kina tsomawa a kwai kina sawa a wuta yana soyuwa, amma kada ki cika wuta, saboda kada kwan ya soyu har yayi baki amma kifin bai soyu ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *