Yadda Ake Hada Alkubus Mai Dan Karen Dadi

Abubuwa Da Ake Bukata

  1. Alkama gwangwani 5
  2. Yeast tea spoon 1
  3. Filawar gwangwani 3
  4. Mai, gishiri da ďan mai.

Abubuwa Da Ake Bukata: Farko zaki kai alkama a niqa miki sai ki tankade da rariyan laushi shima flour a tankade shi a ciki. Sai ki juye yeast a ciki ki zuba ruwa kiyi ta juyawa har sai ya hade sosai. Kwabin kamar na fanke amma yafi fanke tauri sosai. Domin idan ya kumburo kwabin zai saki, don haka da kauri zaki yi shi.

Sai ki rufe a barshi ya tashi sosai. Idan da daddare ne zaki dafa da safe kina tashi ki đan buga shi. In kuma da safe kika yi kwabin zaki yi da rana duk ďaya. Sai a shafa mai a gwangwani a rinka rinka zuba kwabin kamar dai alale. Sai a ci da miyan da ake so bayan ya dahu.

Note: Idan a tukunyar dambu zaki yi ki samu buhu ki saka shi ya zauna a ciki sai ki jera su, ya zama buhun ya hau har sama sai ki rufe duka gwangwanin ki ‘bame da murfin tukunya. Idan kina son yayi kamar cake wato babba guda ďaya duk zaki iya yi in yayi sai ki yanka. In baki da tukunyar dambu ki samu itatuwa ki jera su sai ki saka buhu kamar irin waccen ki jera alkubus ďin a sama ki rufe. Zaki ga ya taso sosai yayi manya. Sannan ba dole bane kiyi da buhu zaki iya yi yanda kike so. Alkaman in so samu ne ki surfe shi kafin kiyi don zai iya miki dussa-dussa. In kin so zaki iya yin na alkama zallah, ko na flour zallah. Bana son alkubus nidai amma na iya 😃😃😃 waďannan pictures ďin ma ba nawa bane.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *