Tambuwal Ya Rantsar Da Sabbin Jagororin Hukumar Zabe Ta Jahar Sokoto

Maigirma Gwamnan Jahar Sokoto Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal CFR (Mutawallen Sokoto) yau Laraba ya rantsarda sabon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jaha tare da mambobin Din-Din guda shida a fadar Gwamnati dake nan Sokoto.

Cikin wadanda aka rantsar akwai Shugaban hukumar, Alhaji Aliyu Suleiman, da kuma sauran mutuane biyar da zasu zama mambobin hukumar : Mu’azu Garba Dundaye, Sidi Muktar Ibrahim, Umar Galadima Durbawa, Abubakar Haliru Dange sai kuma Alhaji Musa Illela.

Gwamna Tambuwal bayan ya taya su murnar wannan jagorancin ya nemi da su rike amana da kuma gaskiya a lokacin gudanarda aikinsu.

Mataimakin Gwamna, Hon Manir Muhammad Dan Iya, Tsohon Minista, Injiniya Bello Suleiman, Kakakin Majalisa, Hon. Aminu Muhammad Achida, Sakataren Gwamnatin jaha, Mallam Saidu Umar FCNA (Mallam Ubandoman Sokoto) kwamishinoni, shugaban ma’aikatan fadar Gwamnati, Alh Muktar Magori da sauran kusoshin gwamnat ne suka halarci wannan taron

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *