Shugaba Buhari Zai Rushe EFCC

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aikawa majalisar dattawan kasar nan bukatar sa na sauya fasalin hukumomin yaki da cin hanci da rashawa da dangoginsu da suka hada da EFCC da kuma ICPC.

Shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan, ya karanta wasikar shugaba Buhari a zauren majalisar, mai taken: “Dokar hukumar gurbattun kudade”.

“Manufofin hukumar shine sa ido kan dokar da kuma yin ruwa da tsaki a alkinta kudaden da aka kwato daga barayin kasa ta hanyar hadin kai da hukumomin tsaro.

Shugaban majalisar ya ce sabuwar dokar za ta magance matsalar rufa rufa da ake yi wajen alkinta kudaden da hukumomin biyu ke kwatowa daga barayin kasa.

Buhari a cikin wasikar ya bayyana cewa aikewa majalisar dattijai bukatar rushe hukumomin da samar da sabuwar dokar ya samu sahalewar majalisar zartaswa ta kasa.

A cewar wasikar da aka aikata a ranar 6 ga watan Oktoba, sabuwar dokar hukumar zai tabbatar da yaki da cin hanci da rashawa, safarar kudade ba bisa ka’ida ba da sauran laifuka.

“Sannan abu mai muhimmanci shine, hukumar za ta tabbatar ‘yan Nigeria sun amfana da kudaden da aka kwato daga mahandaman kasar, ba tare da boye boye ba.”

Idan har aka amince da wannan doka, za ta taimaka wajen dakatar da EFCC da sauran hukumomin yaki da rashawa guda 6 daga rufe asusun mutanen da ake bincika.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *