Rashin Tarbiyya Ya Dawo Arewa

A kullum ina mamakin yadda dan Arewa yake ikirarin cewa shuwagabanninsa na Arewa basu masa adalci, alhali kai kanka bakawa shugabannin naka na arewa adalci ba, ta hanyar nuna misu soyayya kamar yanda ‘yan kudu suke nuna soyayyar su ga nasu shuwagabannin ba.

Yakamata ka tsaya kayi nazari, duk irin kashe-kashen da akayi a lokacin mulkin Goodluck Elebe Jonathan baka taba jin wani Kirista ya fito yana zaginsa ko yunkurin yiwa gwamnatinsa zanga-zanga ba.

Hakama bayan ya sauka mulki baka taba jin wani Kirista ya fito yana sukarsa ba, saboda kasancewar kan su hade yake, duk yadda Kirista ya lalace bazaka taba jin Kirista dan uwansa yana zagin sa ba.

Amman abin mamaki mu a nan Arewa inda mu ke da shiriya ta addinin musulunci sai kaga karamin yaro yana zagin shugaban kasa Muhammadu Buhari, zagi irin wanda addinin musulunci ya haramta. Wanda nake ganin ko wannan kadai ya isa ya janyo mana wata babbar musifa a Arewacin Najeriya.

Yakamata dan Arewa ka yiwa shugaban kasa Muhammadu buhari uzuri da kuma addu’ar samun nasarar ganin bayan wadannan makiyan Arewacin Najeriya dake kokarin ganin sun hana shi taimakawa Arewacin Najeriya ta hanyar yi masa zagon kasa, makirci, sihiri, zamba cikin aminci da sauran su.

Yakamata ka ajiye maganar adawar siyasa gefe, ka sani cewa ko naka dan takara ya zama shugaban kasar nan haka zasu masa irin wannan zagon kasa da sukawa shugaba Muhammadu Buhari.

Buhari gyara ne yazo ya yi, sannan wannan gyara daya zo ya yi ya bai samu hadin kan manyan kasar nan ba, bai samu hadin kan ‘yan arewa ba ballantana ‘yan kudu.

Ubangiji Allah ka yaye mana wannan musifa.

Ubangiji Allah ka shirya al’ummar mu na Arewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *