Makulashe: Yadda Ake Hada Suya (Tsire)

Abubuwan Da Ake Bukata:

  1. Nama, borkono, kuli-kuli, citta, kimba, kanunfari, masoro, thyme, curry, busashen tafarnuwa da sauran spices. Mangyada, gishiri, maggi sai tsinkin tsire.

Yadda Ake Hadawa:

Ki daka dukkanin spices naki tare da kuli, amma kulin ya ďan fi yawa, kuma ki sanya maggi da gishiri. A zabi nama mai kyau wanda babu kitse sosai a jiki, sai ki yanka shi sirara ta kwance da dan tsayi kadan sai ki ďauko tsinken tseren ki jera wannan naman a jiki. Wato in kin huda ta ciki sai ki fitar da shi ta waje.

Daga nan sai ki sami kwano ki zuba mangyada dai-dai misali tare da gishiri da maggi kaďan ki shafe jikin naman duka. Kina yi kina sanya shi cikin haďin kulin ya kama jikinsa da kyau. Daga nan in a oven ne sai ki yi ta jera su suna gasuwa. In ma a rushi ne duka ba damuwa.

Tsire fa shine amarya tashi watssake 😃

Idan an je siya a rinka hana su sanyawa cikin newspaper domin yana da rubutu a jikinsa. Kuma wasu likitoci sun ce yana haddasa ciwon kidney (qoda) Allah Ya kare mu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *