Makulashe: Yadda Ake Hada Alkaki

Kayan Hadi:

  1. Alkama mudu ďaya
  2. Sugar gwangwani 6
  3. Nono na shanu N100
  4. Man shanu ďanye N100
  5. Butter simas rabi
  6. Mai kwalba biyu

Yadda Ake Hadawa : A sheqe alkama a cire dukkan dattin ko a wanke a baza shi a rana ya bushe. Sai a kai babban inji a mishi ‘barjin fate idan aka dawo dashi a bude tsakiyar alkaman a kwanon kwabi a juye nonon shanu, butter, man shanu, sai a murje shi da kyau ya hade. Sai a zuba ruwa amma kwabi zaki mishi mai qarfin gaske yanda zai hade da kyar, Sai a rufe shi ya kwana.

Idan kika tashi da safe sai ki jiqa kanwa, ki rinqa yayyafa masa kina hadashi kina bugawa. Har sai kin diba a hannun ki kin masa naďin alkaki kin ga bai karye ba. Wato kin yi tsaho dashi kin murza duka bai karye ba. Kin ga ba qaramin bugu zaki masa ba. Ba a jibga masa ruwa sam, yayyafa masa zaki rinqa yi kina buga shi.

Sai a zuba sugar a tukunya, a zuba ruwa kamar kofi uku a ďaura a wuta. Idan mai buqatar sugar alkakin ya rinqa ďiga ne bayan ya gama shiga cikin sa sai ki saka tsamiya kwaya đaya ko table spoon na lemun tsami yayin da kike dafawa. In kuma kina son ya bushe a jikin sa kamar nawa to kada kisa.

Wurin dafa sugar a kula yana fara yin kumfar farko na dahuwa a ďiba a cokali yana ďan fara shan iska zaki ga yayi danqo. Sai a sauke don haka kada ki barshi yayi ta dahuwa kamar na tuwon madara ko aya.

Sannan wurin soya alkakin a saka mai aqalla kwalba biyu ko fiye, baya shan mai sam amma yana buqatar mai wurin soya shi. Kuma wutan kadan-kadan yanda cikin zai soyu. Bayan kin tsane shi a mai straight a cikin sugar zaki saka, idan kina gabda tsamewa sai ki kwashe na cikin sugar ki sa a kwanon da zaki ajiye.

Abun Kulawa: Idan kin yi wanda baki so sugar yana bin sa ne zai ďan rinqa daskarewa sai kina yi kina ďan narkar dashi. Sannan ludayin da zaki rinqa amfani dashi wurin suya daban, na sakawa a sugar shima daban. Masu tambaya akan abun da basu gane ba zasu iya yi. Wainda basu iya yin naďin shi ba su nemi wainda suka iya su koya musu. Zaku ga wasu alkakin su yayi ja wasu sun yi haske yanayin alkaman ne amma babu damuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *