Kwalliyar Abinci Da Kuma Tsara Shi

Yana da kyau ko wacce mace tasan bayan tayi wa maigidan ta ko bakin ta abinci mai dadi, to fa tsara abincin a plate ko a flask yana da mutukar muhimmanci, domin idan aka tsara abinci tun a ido kawai mai shi zai kosa ya kai shi cikin bakin sa. Kuma zai sa mijin ki yaji cewa lallai kina kayatar dashi da sababbin abubuwa kullum.

Mata dayawa suna kokarin yin abinci mai dadi amma gaskiya suna kwafsawa wurin tsara shi. Tana gama abinci yaba shi kawai take yi anyhow, sai ka ga an dai ci ne kawai amma baya bada tsari yanda ya dace.

Idan kika tashi yanka fruits, ya kamata ki dan yi decoration yanda zai bada ma’ana. Misali a pictures na kasa zaku ga yanda aka tsara fruits dinnan, to ko da baki iya kamar wainnan ba yana da kyau kiyi yanda zai bada sha’awa.

Sannan haka ko abincin gargajiya ne ki dan masa tsari kamar yanda aka yi a wainar can dama sauran abincin. Sannan ko da drink ne a cup yana kyau ace kin dan masa kwalliya kamar yanda pictures suka nuna.

Domin a farantawa wainda ake yi don su.

Yar’uwar ku Sadeeya Lawal Abubakar
Zauren Girke-Girke.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *