INEC Zata Dauki Matasa Dubu 3000 Aiki Domin Zaben Maye Gurbin Kujerar Sanatan Imo

Hukumar Zabe Mai Zaman kanta zata dauki mutum 3000 aiki, domin su gudanar da Zaben Kujerar Sanata mai Wakiltar yankin Arewa na jahar Imo wanda za’ayi a ranar 31 ga watan Oktoba.

Hakazalika Jam’iyyu 14 masu rajista aka baiwa damar fafatawa a zaben maye gurbin Kujerar Sanata mai wakiltar yankin Okigwe

Kwamishinan Zaben Jahar Imo Farfesa Francis Ezeonu wanda ya bayyana haka a yau Laraba a lokacin taron tattaunawa a Okigwe, yace Sakamakon Zaben za’a rika turashi a adireshi na yanar gizo na Hukumar.

A cewar shi, yan takara 14 jam’iyyun su suka gabatar wa Hukumar domin su fafata a zaben.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *