Ƴan Daba Sun Tarwatsa Zanga-zanga Matasa Tare Da Ƙwace Musu Wayoyi A Kano

Ƴan daba dauke da makamai sun tarwatsa matasan da suka fito zanga-zanga kan matsalar tsaro da ake fama da ita a arewacin Najeriya.

Yan daba sun tarwatsa masu zanga zangar ne a daidai titin kabuga da ke ƙwaryar birnin tare da kwacen wayoyi.

Wannan yanayi ya tilasta wa masu gangamin hakura da ci gaba da tattakin.

Ko a jiya ma sai dai aka samu irin wannan matsalar a Abuja da kuma Legas, inda matasa dauke da makamai suka kai hari kan masu gangamin EndSars.

Lamarin na jiya ya yi sanadi rayuka da jikkata mutane da dama da kuma farfasa motoci.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *