Haɗarin Dake Tare Da Baiwa Saurayi Budurcin Ki Da Jikin Ki

YAN’MATA SAI A KIYAYE…..

A makon data gabata kadai na samu korafe korafe na yan matan da suka yi sakaci suka bada gabansu da zmudin za a aure su. Daga bisani kuma samarin ko mazan suka ci suka ware.

A duk lokacin da na hadu da budurwa idan muna hira na kan jawo hankali su akan kada su sake su bada gindin su da saran namiji zai aure su yin hakan ba karamin ganganci bane da zai iya sanadiyar lalata musu rayuwa.

Maza masu karanci shekaru masu aure da ma wadanda basu taba aure ba sune aka fi samu da irin wannan cin amanar. Saboda akasarin irin wadannan mazan suna da tunanin duk macen da suka ci bata cancanci su aure ta ba koda kuwa sune suka soma lalata mata rayuwa. Don haka da zaran sun biya bukatar su sai sun akauda zancen auren a gefe idan ma anyi rashin sa’a ciki ya shiga basu cika yarda sune suka yi wannan cikin ba.

Duk da irin wannan halin da irin wadannan mazan ke nunawa yan mata masu kananan shekaru a kullum rashin wayewar kan irin wadannan mata sai dada karuwa yake yi. Sakaci da sakarcinsu sai yawaita suke yi. Kullum suna shiga mugun hannu da zummar za a aure ta amma daga bisani a cita a barta.

Irin Haɗarin da wadannan yan matan suke fuskanta bayan mayaudaran mazan nan sun samu galaba akan su yana da yawa.
Wasu matan daga wannan lokacin kuma sai su zarce zinace zinace bayan wannan saurayin ya gudu. Hakan nan duk wanda wannan Saurayin da yayi lalata da ita yasan ya sanya zai yayata musu shifa ya gama da ita suma su je su kwashi rabonsu. Daga wannan lokacin zata ga duk wanda ya zo mata baya mata zancen aure sai dai zancen zina saboda yasan tasan maza.

Akwai kuma wasu matan da suke nacewa sai sun ci gaba da soyayya da mazan da suka lalata su suka fasa auren nasu. Hakan kuma bazai haifar mata da komai ba sai dai ya ci gaba da zina da ita tunda ya fadamata babu zancen auren amma taki yarda.

Idan aka duba da kyau yan matan da suka fandare suka shiga duniya da karancin shekaru asalin hakan samarin banza ne. Masu cinsu suki auren su. Masu Koya musu shaye Shaye.

Ana samun irin wannan halin wajen dattawa maza amma ba kasa fai ba. Shi dan iskan dattijo tun a farko ma zai nuna miki babu zancen aure tsakanin ku sai dai idan kece kika kwallafa rai akansa. Haka kuma shi mazinacin tsoho yin zina da mace bai hana shi aurenta ba kamar maza masu karancin shekaru ba. Cikin sauki namiji da ya manyanta yana miki ciki zai amsa ba tare da ya ja zance da tsawo ba.
Sai dai ba ina nufin ki guji masu kananan shekaru kuje kuna zina da tsoffi bane. Bambamci tsakanin su muka kawo muku.

Duk namiji dake sonki da gaskiya zai iya hakuri na tsawon lokacin da zaku dauka kamin kuyi aure. Idan kuma aka samu kuskure kuka afkawa juna, namiji mai sonki bazai guje ki ba saboda yayi zina dake.
Yana da kyau mata musamman masu karanci shekaru su daina amfani da zuciyar su aokacin da suke soyayya, su rika amfani da hankalin su ta nan ne idan na miji yace miki zai ya soma cinki zai aureki kina iya ce masa kin haura da soyayya. Amma ba ki bashi jikin ki ba wai da sunan kada ya gudu ya auri wata daga baya ya maida ki karuwar gida.

Mata masu karancin shekaru musamman sabbin balaga da zaran sun soma soyayya da samari babu abun da ke ransu illa aure da wannan koma yaya yake. Wannan yana cikin wasu hanyoyim dake jefa su dana sani. Ki sani shi aure ana yin sa ne domin zama na har abada ba na wani lokaci ba. Samun mijin da zaki zauna dashi zama mai daurewa kuma bada zumudi ake samunsa ba cikin natsuwa ake iya fahimtar sa. Ba da zafin soyayya ake gano sa ba sai ansa hankali.


Allah Ya shirya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *