Yadda Ake Dafa Soyayyiyar Shinkafa Wato Fries Rice

Abubuwan Da Aka Bukata:

  1. Kaza , shinkafa , peas, karas , koriyar wake , albasa, hanta, oil, kayan Kamshi kamar su Curry sauran spices and seasonings.

Yadda Ake Hadawa :

Ki gyara kaza ki zuba mata ruwa ya ďara yanda zata dahu kadan. Ki zuba dukkan spices da dandano. Ki daka ko niqa albasa ki juye a cikin kazan amma zaki iya yanka wa ba damuwa. Sai ki rufe ta dahu yanda kike so. Ki yi per boiling shinkafa ki wanke ta, idan namanki ya dahu sai ki tsame shi daga cikin ruwan naman. Ki samo rariya ko wani abu ki tace ruwan naman. Ya zamana duka dattin spices kin cire shi a ruwan. Sai ki mayar da tukunya a wuta ki juye ruwan da kika tace, ki qara ruwa dai dai yanda zai shanye kan shinkafan kadan. Saboda so ake yi ta yi taushi amma kuma a qame, wato bata cabe ba ko kadan. Kenan sai kin yi aiki da kwakwalwa wurin zuba ruwan, daga nan sai ki qara curry saboda yayi wannan yellow, sai ki qara su maggi da gishiri da spices idan basu da duhu sosai. Wato ba zasu sanya ruwan yayi baqi kamar na jollof ba. Sai ki jujjuya ki dandana sai kin ji komai ya fito yanda kike so kuma kike ganin zai kama shinkafan. Yana dan tausowa sai ki juye shinkafan. Ta qara sa dahuwa ki sauke.

A gefe kuma kin tafasa dukkan vegetables bayan kin yanka, wato sun yi taushi musamman peas saboda yana da dan qarfi. Kin kuma tafasa hanta kin yanka shi shape da kike so, ki yanka albasa qanana. Sai ki daura tukunyar suya a wuta.

Ki daidaita wutan, sai ki debi mai dan dai dai ki zuba saboda ba a cika mai yar’uwa a fried rice. Sai ki fara zuba albasa, in ya dan soyu sai ki zuba hanta, ki jujjuya shima ya dan soyu sannan ki zuba vegetables. Ki jujjuya suma su dan sha wuta kadan sai ki debo shinkafan ki zuba ki cigaba da soyawa. Ko wane kwayar shinkafa ki tabbata wuta ya dan tabe shi. Kada ki cika juyawa da yamutsawa sosai. Shi yasa nace ki saisaita wutan ki. Haka zaki yi ta yi har sai ta soyu, zaki ga ta yi wara wara abinta. The same method zaki bi in kin kwashe zaki sake soyawa wani. Saboda kada ki ce lokaci daya duka zaki juye ki soya sai dai in shinkafar kadan ce. Amma a hankali zaki yi ta soya wa kuma ki rinka dai dai ta komai. Kada ki laftama wannan kaya wani suyan kuma babu kayan da zaki zuba. Kina fara soyawa qamshi ma kawai ya ishi mutanen gida.

Ita kuma kazan sai ki soyata sama sama, in kin tsane ta sai ki jajjaga tattasai da tarugu. Ki dan yanka albasa kadan, ki soya albasan da mai kadan sai ki juye tarugu da tattasan, sai ki dauko wancan dattin kazan da kika tace ki juye a ciki. Wato wannan albasa da burbushin kazan da kika tace ba zubarwa zaki yi ba. Sai ki dan zuba ruwa kadan, ki qara dandano yaji, sai a dafa shi kamar miya. Amma yayi romo romo, sai ki juye kazan a wata tukunya ki zuba mata wannan kayan miyan ki jujjuya. Kin san akwai dan romo romo sai ki sa wuta kadan kadan ki rufe. Kina yi kina juyawa, ruwan zai qame a jikin kazan kuma kayan miyan ya kama kazan itama. Ta yi zaqi da dadi.

In so samu ne fried rice ki mata coleslaw, saboda kun ga ita ba a sanya mata kayan miya. Cin ta zallah haka nan ba dadi sosai, don haka ko dai mutum yayi pepper meat mai miya miya. Ko kuma ki soya kazan sai ki yi coleslaw. Daga nan sai ki yi serving mai gida ko baqi.

Note: Mata fried rice ba wani abincin duniya bane, mata da yawa sai ka ji sun ce su basu iya fried rice ba a koya musu ai abincin da wuya. Wannan shine simplest way na making fried rice. Jollof ya fi mun shi wuya, shi aikinsa kawai yanke yanke ne da soye soye. Ki bi wannan tsarin ki gani tsaf zaki yi kowa yayi santi. Ki yi surprising mai house. Namu na gida wallahi ya fi na restaurant din da suke zuwa su siyo, ka ji ya maqale maka a wuya saboda karfi ga tsada. Kuma ki dafa shinkafar ta yi taushi kada ki yi ta kamar tsaba. Iyaka dai kada ki yarda ta cabe miki. Don haka ki gwada, in kin samu problem ki zo ki tambaye ni na gyara miki har ki kware. Ki fara gwada wa da dan kadan. Ki bar maganar wasu egg fried rice ko chicken fried rice. Ki fara iya wannan din tukuna sai mu kama next step.

🖎Sadeeya Lawal Abubakar.

ZAUREN GIRKE-GIRKE.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *