Maganin Asma Kaifiyyan (Asthma)

Kamar yadda a baya mukai bayani akan maganin ciwon Asma kuma jama’a da dama sun jarraba wasu ma sun kira ni a waya bisa samun dacewa da sukai Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah.

A yau ma ga wata fa’ida wacce tana da tasiri sosai wajen magance wannan cuta cikin yardar Allah.

ABINDA ZAA NEMA.

  1. Kwallon mangwaro(Mango Seeds)

Zaa nemi kamar guda 5 sai a bare cikin sa,akwai wani kwallon a ciki to zaa shanya ya bushe,amma baa shanyawa a cikin rana sai inuwa ko inda babu rana.

Idan ya bushe zaa dake shi sosai sannan a samu zuma amma mara hadi ake so, sannan a kwaba da wannan garin kwallon zaa rika shan chokali 1 a ruwan tea ba madara ko a ruwan dumi.

Sau biyu a rana safe da dare tsawaon sati 3 insha Allah zaa dace

Wallahu a’alam

LIKE AND SHARE ➡️.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *