Amfanin Ganyen Magarya Da Garin Magarya Ga Lafiyar Dan Adam.

Bismillahi Rahmanir Rahim.

Itaciyar magarya wadda akafi sani da (Assidir) a larabce kuma (Lote) a turance, itaciyace mai albarkatun da dadewa Annabi S.A.W ya tabbatar da amfaninsa.

Magarya yana kunshe da magunguna masu matukar mahimmanci ga jikin dan Adam kuma yana da karfin kashe kwayoyin cuta cikin dan kankanin lokaci.

Magarya Antibiotic ne mai karfin gaske kuma cikin ikon Allah bashi da wani illa wato side effects na azo agani.

KADAN DAGA CIKIN AMFANINTA.

1.Ciwon daji (cancer) :
Idan anadafa garin magarya ana sha da zuma yana kashe kwayar cutar daji koda a cikin jini ne idan kuma Yayi miki sai arinka dafavgarin magaryar da ruwan khal ana wanke wurin mikin idan an wanke sai a barbadavgarin magaryar.

  1. Yana da karfin yaqar cutarfata kamar su tautau, makero,Karzuwa da sauransu

A kwaba shi da zuma arinka sha Ana shafawa a Wurin da abin ya shafa.

  1. Yana tsaftace jini domin Yana dauke da sinadarin Saponin,alkaloid da triterpenoid wadannan Sinadarai ne masu tsaftace Jini.
  2. Shansa da ruwan zafi yana magance gajiya da ciwon Jiki.
  3. Yana magance ulcer idan ana shansa da madara ko zuma.
  4. Yana taimakawa hanta ya hana shi jin ciwo da cututtuka.
  5. Yana daidaita nauyin mutun.
  6. Yana tsaida zawo cikin kankanin lokaci idan aka Shashi da ruwa ko koko.
  7. Yana miqar da kasusuwa musamman gamai karaya.
  8. Yana maganin rashin shaawa ga mata idan suna tsarki dashi kuma Suna shansa da madara.
  9. Kuma a karshe dai yana warware sihiri a cewar malaman sunna Idan aka jika garin a ruwa tare da karanta wasu ayoyi daga cikin Alqur’ani mai girma.

Allah yasa mu dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *