Siyasa: Milyoyin Ƴan Najeriya Na Cikin Matsanancin Talauci – Yemi Osinbajo

Mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo ya yarda cewa milyoyin ƴan ƙasar nan na cikin matsanancin talauci.

Ya ce zaɓaɓɓun shugabanni zai kasance ba su da amfani idan ba su hada kai wajen shawo kan matsalolin da ke barazana ga rayuwar ƴan ƙasar nan.

Osinbajo ya shaida hakan ne a wani taron kwana biyu kan shugabanci da ake gudanarwa a fadar gwamnati da ke Abuja.

Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma shaida cewa akwai bukatar bangaren majalisa da zartarwa su yi aiki tare muddin ba sa son su gaza a idon ƴan ƙasar da suka zaɓo su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *