Sarki Ahmed Nuhu Bamalli, Sarkin Zazzau Na 19 Ya Halarci Sallar Juma’a A Babban Masallacin Abdul-Kareem Dake Zaria

A yau ne alummar masarautar Zazzau suka tsunduma aka taru a babban birnin domin halartar jam’in Sallar Juma’a tare da sabon Sarkin Zazzau na 19, Alhaji (Amb) Ahmed Nuhu Bamalli.

Daga 7 ga watan Oktoba 2020 ranar da aka sanar tare da kaddamar da shi a matsayin Sarki, al’ummar masarautar zazzau na ta murna kowa na ta garzayawa zuwa fadar Sarki domin mika gaisuwa ban girma da kuma goyon baya ga mai martaba sabon Sarkin Zazzau.

Al’ummar sun taru kuma babu shakka wannan rana za a ta bada labarinsa a tarihin masarautar a matsayin ranar da jikan Sarkin Zazzau na farko, Mallam Musa, ya hau karagar mulkin da kakansa ya bari shekaru 100 da suka gabata. Wanda hakan ya sa shine mutum na farko daga daular Mallawa da ya hau karagar mulki tun shekarar 1920 ( Shekaru 100 da suke gabata) bayan mulkin Sarki Aliyu Dan Sidi.

Babu shakka wannan rana ne wanda yake kunshe da farin ciki, da murnar, da jin dadi tare da nishadi wanda ya ke nuna al’adun masarautun Hausa Fulani ta hanyar zaman lafiya da juna tare da girmamawa shugabanni. Wannan ranar farin ciki ne ga duk alumma sannan kuma muna masu godiya ga ubangijin Allah a kan Rahamarsa da ya mana a matsayin mu na bayinsa.

Muna masu rokon Allah ya taya shi riko sannan kuma ya kasance alheri gare shi da kuma masarautar Zazzau. Allah ya ja zamaninthe Sarki Mai Zazzau #amin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *