Ranar Shanyewar Ƙwaƙwalwa ta Duniya

Ko mene ne shanyewar ƙwaƙwalwa?

Larurar shanyewar ƙwaƙwalwa ko dakushewar ƙwaƙwalwa wacce ake kira da “cerebral palsy” a turancin likita. Shanyewar ƙwaƙwalwa larura ce da kimanin mutane miliyan 17 ke fama da ita a faɗin duniya. Kuma ita ce larura mafi nakasa yara yayin girmansu. Wannan matsala ce da ta fi shafar motsin gangan jiki, magana, gani, da sauransu sakamakon shanyewar ƙwaƙwalwa.

A jiya ne, wato ranar 6 ga watan Oktoban kowacce shekara ake bikin ranar masu larurar shanyewar ƙwaƙwalwa domin nuna irin nasarori da ci gaban da masu larurar suka samu a ƙoƙarin dogara da kansu wajen ayyukan yau da kullum, da ma zaburar da iyaye, al’umma da mahukunta domin tallafa musu da hanyoyin da za su inganta da sauƙaƙa rayuwarsu.

Yawancin yaran da matakan girmansu ke tafiyar hawainiya suna fama da shanyewar ko dakushewar ƙwaƙwalwa ne saboda raunin da ke samun ƙwaƙwalwarsu kafin ta gama girma kamar:

 1. Yayin rainon ciki: misali,
 • jirkicewar jigidar ƙwayar halitta,
 • haihuwar bakwaini, da sauransu.
 1. Yayin haihuwa: misali,
 • doguwar naƙuda,
 • shaƙewar jijiyar jinin cibiya yayin naƙuda,
 • shawara,
 • matsanancin zazzaɓi, da sauransu.

Haka nan, jariran da ba su yi kuka nan take ba bayan haihuwarsu na da haɗarin samun wannan matsala.

 1. Bayan haihuwa: misali,
 • sanƙarau,
 • zazzaɓin cizon sauro mai ratsa ƙwaƙwalwa.

Alamomin shanyewar ƙwaƙwalwa sun haɗa da:

1) Kasa iya motsa sassan jiki; saboda waɗansu yaran jikinsu ba shi da ƙwari, waɗansu kuma jikinsu ko gaɓɓansu kan rirriƙe ne. Misali, waɗannan yara kan gaza iya riƙe wuya, zama, rarrafe, tsaiwa ko tafiya a watannin da ya kamata su cimma waɗannan matakai.

2) kasa iya magana/furuci.

3) Dalalar da yawu/miyau.

4) matsalar gani, juyewar ido ko hararagarke.

5) matsalar cin abinci da sauransu.

Abubuwan da ya kamata ka sani game da yara masu larurar shanyewar ƙwaƙwalwa sun haɗa da:

1) Ɗaya cikin yara huɗu ba ya iya yin furuci/ magana.

2) Ɗaya cikin yara uku ba ya iya tafiya da kansa.

3) Ɗaya cikin yara biyu na da dakushewar kaifin basira.

4) Ɗaya cikin huɗu na da farfadiya.

Wani abin takaici shi ne yadda wasu iyayen ke tunanin wai irin waɗannan yara aljanu ne suka taɓa su, ko suka shanye musu gaɓoɓi, ko kuma wai suna da taɓin hankali ne. Wannan sam ba haka bane! Wannan ya kan sa a bar yaran a gida ba tare da kai su asibiti ba, wanda hakan zai sa yaran har su nakasa.

Muna ƙara jinjinawa iyayen yara masu wannan larura da irin ƙoƙarin da suke yi ba gajiyawa wajen zuwa asibiti. Muna sake kira da kada a gajiya ganin cewa ba a samun ci gaba cikin gaggawa. Ya kamata a sani cewa wannan matsalar ba a shan magani a warke nan take. Saboda haka, haƙurin ziyartar asibiti akai-akai ita ce mafita.

Likitocin fisiyo (Physiotherapists) na gaba-gaba wajen tallafa wa rayuwar waɗannan yara domin su sami mafi ingancin rayuwa domin g
dogara ko kula da kansu.

Garzaya da yaro asibiti da zarar an lura da matakan girmansa na tafiyar hawainiya, ko kuma bayyanar wasu daga cikin alamomin da aka ambata a sama domin ba shi kulawa ta musamman.

WorldCerebralPalsyDay2020

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *