Yajin Aikin Da Muke Yi Zai Yi Tsawo Matuƙa— ASUU

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya, ASUU, ta ce ba za ta dawo aiki ranar 12 ga Oktoba, 2020 ba, kamar yadda Gwamnatin Tarayya ta sanar cewa jami’o’in gwamnati su dawo aiki biyo bayan sassauta dokar kullle da aka ƙaƙaba don daƙile COVID-19.

ASUU ta bayyana haka ne ta bakin Shugabanta na Ƙasa, Farfesa Biodun Ogunyemi a wata tattaunawa da jaridar PUNCH.

Mista Ogunyemi ya faɗa wa PUNCH cewa Gwamnatin Tarayya ba da gaske take yi ba game da tattaunawa da ƙungiyar, yana mai ƙarawa da cewa malaman jami’o’i ba za su dawo aiki ba tare da wani alƙawari ba.

Ya ambaci musamman Akanta Janar na Ƙasa, Ahmed Idris, bisa yadda ya yi watsi da umarnin Shugaba Muhammadu Buhari da ya ce a biya malamai albashinsu, yana mai ƙarawa da cewa ‘yan Najeriya su shirya ganin “yajin aiki mai tsawo” a jami’o’i duba da yadda gwamnati take ɗaukar batun.

Ya ce: “Kar ka yi zaton mutane za su koma ofisoshinsu ba tare da wani alƙawari ba.

“Kar ka sa ran mambobina su dakatar da wannan aiki idan ba a biya buƙatunsu ba.

“Mataki ne a fili da kowa zai yi a wannan yanayi”.

Tun a watan Maris ne mambobin ASUU suka fara yajin aiki don nuna rashin amincewarsu bisa shirin Gwamnatin Tarayya na sa su a cikin Tsarin Biyan Albashi na Bai Ɗaya, wato IPPIS.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *