Yadda Makarantun Furamare A Kano Su Ka Koma Gurin Kwanan Jakuna (Hotuna)

A daidai lokacin da ya rage saura kwanaki biyar ɗalibai su koma makaranta a faɗin jihar Kano, bayan sun shafe fiye da watanni 5 a zaune a gida sakamakon annobar COVID-19.

Sai ga shi ƙungiyar iyayen ɗalibai da malamai ta garin Guringawa da ke yankin ƙaramar hukumar Kumbotso, ta bukaci gwamnatin jihar Kano da ta kawo musu dauki sakamakon Jakuna da su ka mayar da ajujuwa wurin kwana da ruftawar sili har ta kai ta kawo wani wuri na rushewa a jikin bangon ginin saboda rashin rufi.

Wannan koken yana zuwa ne a lokacin Gwamnatin Kano ta ce za ta kashe fiye da naira miliyan 880 domin gyara wasu makarantun Firamare a ƙananan hukumomi 44 da ke jihar.

Idan za a iya tunawa dai tun bayan rantsar da gwamna Abdullahi Umar Ganduje a zangon mulki na biyu yayi alkawarin bayar da ilimi kyauta a jihar Kano, kuma tilas ga kowa da kowa.

Haka kuma a cikin watan Janairun shekarar da mu ke ciki ne majalisar dokokin jihar Kano ta amince wa gwamna Abdullahi Ganduje ya ciyo bashin Naira biliyan 15 domin inganta fannin ilimi a jihar Kano.

Ga Hotunan A Kasa;

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *