Hotuna: Sanata Danjuma Goje da Amaryarsa Aminatu Dahiru Binani

Tsohon gwamnan jihar Gombe, Sanata Muhammad Danjuma Goje tare da amaryarsa Aminatu Dahiru Binani. 

An dai ɗaura auren ne a ranar juma’ar makon jiya, a birnin tarayya Abuja.

Ɗaurin auren ya samu halartar manyan mutane waɗanda su ka haɗa da shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmed Lawan; Gwamna jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahaya, da takwaransa na jihar Kano, Abdullahi Ganduje, da Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha. 

Sauran su ne Ministan Sadarwa, Dr Isa Pantami, da tsohon gwamnan jihar Benue Sanata Gabriel Suswam, da tsohon gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Adamu da sauran fitattun mutane. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *