Zulum ya roƙi Buhari ya gayyato sojojin Chadi su taya Najeriya yaƙi da Boko Haram

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya nemi Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gayyato sojojin kasar Chadi, domin su taimaka a yakin da ake yi da mayakan Boko Haram a yankin Tafkin Chadi.

Wannan na zuwa ne bayan da Gwamna Zulum ya tsallake rijiya da baya har karo uku, wanda ake zargin mayakan Boko Haram ne suka kai wa kwambar motocin sa harin kwanton bauna.

A cewar gwamna Baba Gana wannan dai na nuna irin yadda ayyukan ta’addanci ke kara tsananta a yankin arewa maso gabashin kasar nan, wanda kuma ya zama wajibi a kara zage dantse wajen dakile ayyukan su.

A cikin watan Janairun shekarar nan ne ƙasar Chadi ta janye sojojin ta daga yarjejeniyar gangamin yaki da Boko Haram da aka kulla da ita a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *