‘Yan Bindiga Sun Yi Ajalin Jami’in Kwastam A Katsina

A ranar juma’ar da ta gabata ne ya bindiga suka yi ajalin Garba Nasiru mai mukamin mataimakin sifirtanda na hukumar hana fasa-kauri(Customs)…

Yan bindigar, sun farmaki gungun jami’an ne a dai-dai wurin tsayawar su na kauyen Dan Arau dake kan hanyar karamar hukumar Jibia zuwa Birnin Katsina….

Anyi musayar wuta ta gaske, tsakanin jami’ai da yan bindigar gabanin kwatar gawar Garba Nasiru daga hannun yan bindigar, jami’in hulda da jama’a na hukumar yan sandar jihar Katsina Gambo Isah ya tabbatar da faruwar lamarin….

Haka zalika dai, a ranar Lahadin da ta gabata ne yan bindigar sunyi garkuwa da kimanin mutane 20 dake aikin gona a garin Mallamawa dake yankin karamar hukumar ta Jibia….

Duk da kokarin gwamnatoci wajen ganin an kawo karshen matsalar tsaron jihar ta Katsina, kawo yanzu talakawan jihar na fuskantar barazana to firgici silar zafafar ayyukan yan bindigar a kullum, wanda kwanakin baya kananan hukumomi 10 na yankin kudu maso yammacin jihar ne kurum ke fama da matsalar, yanzu kuwa kusan a iya cewa babu tabbatace wuri a jihar da zaka je hankali kwance ba tareda fargaba ba…

Muna rokon Allah ya kawo mana sauki a lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *