Kuskure Ne Babba Hasashen Tarwatsewar Najeriya – Lamiɗo

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya soki lamirin mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo kan zargin yin magana game da ballewa da rabuwar Najeriya.

An ruwaito cewa Lamido ya kuma caccaki Babagana Zulum, da dattawan kasar, Cif Edwin Clark, Cif Ayo Adebanjo, Janar Theophilus Danjuma da sauran mutanen da suka yi sharhi makamancin wannan kan ballewar Najeriya.

Sule Lamido ya bayyana hakan ne a cikin sakonsa na bikin cikar Najeriya shekaru 60 da samun yancin kai.

Tsohon gwamnan ya yi zantuka masu taba zuciya kan hadin kan Najeriya, cewa kada kasar ta kuskura ta balle duk da banbancin ra’ayi.

Ya ce ya zama dole shugabannin Najeriya su san cewa Najeriya ta yi masu rana tsawon shekaru masu yawa.

Sannan ya ce hakkinsu ne su saka wa kasar ta hanyar tabbatar da ganin cewa ‘yan baya masu tasowa ma sun cimma mafarkinsu a karkashin kasa daya.

Rahotannin baya sun nuna cewa Osinbajo ya koka cewa akwai baraka a harkar shugabancin Najeriya da ka iya kawo ballewar kasar har sai an dauki matakin gaggawa.

Osinbajo wanda ya samu wakilcin Boss Mustapha, babbar sakataren tarayya, ya bayyana hakan a ranar Lahadi, 27 ga watan Satumba a Abuja.

Sai dai, Mustapha ya ce an yi wa furucin nasa a madadin Osinbajo mummunan fahimta.

Mustapha ya ce mataimakin shugaban kasar na ci gaba da jajircewa don ganin Najeriya daya.

Har ila yau ya bayyana cewa yana godiya ga kokarin shugaban kasa Muhammadu Buhari a wajen karfafa hadin kan kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *