Korona: Mutum 9 Ne Su Ka Rage Masu Ɗauke Da Cutar A Kano

Gwamnatin jihar Kano ta sallami karin mutane 5 wadanda suka warke daga cutar Covid-19, tana mai cewa a yanzu haka mutane 9 ne kadai suka rage masu jinyar cutar a nan Kano.

Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ce ta tabbatar da hakan ta shafin ta na Twitter, inda ta kara da cewa a jiya Litinin, an yiwa mutane 15 gwaji, kuma cikin su ba’a sami ko da mutum guda mai dauke da cutar ba.

A kasa baki daya kuma an sami karin mutane 120 da ke dauke da cutar, inda jimillar masu fama da ita a yanzu haka ya kai dubu 59,465, cikin su kuma an sallami guda dubu 50,951 sai guda 1,113 da suka rasu a dalilin cutar.

Madogara: Freedom Radio Nigeria

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *