Korona: Annobar Ta Raba Mutum 10,000 Da Aiyukansu A Jihar Kano

Wani ƙiyasi da ƙungiyar masana’antu ta ƙasa reshen jihar Kano da Jigawa ya bayyana cewa annobar cutar korona ta raba mutum dubu goma da ke aiki a masana’atu daban-daban da aiyukansu a jihar Kano.

Shugaban ƙungiyar masu masana’antu reshen jihohin Kano da Jigawa, Malam Sani Hussain ne ya tabbatar da haka a lokacin da ya ke tattaunawa da jaridar Nigerian Tracker.

Malam Sani Hussain ya ce masana’antun da ke jihar Kano sun shiga halin tsaka mai wuya a lokacin dokar kulle, wanda hakan ya sanya ala dole su ka rufe masana’antun.

Ya ƙara da cewa a lokacin da aka ɗage dokar kulle a jihar Kano da sauran maƙotan jihohi, masana’antu sun dawo su na ɗan yin aiki sama – sama, wanda hakan ya sanya masana’antu ba sa iya yin aikin da zai kai su ga cimma ƙudurinsu na samarwa tare da sayar da kayayyakin da su ka sarrafa a shekara.

Hakazalika Malam Sani Hussain, ya ce a bisa wannan dalili ne ya sanya masana’antu faɗuwa a harkar cinikayyarsu, domin kudin da su ka sanya wajen samar da kaya ba ya dawo musu da riba.

Shugaban ya ƙara da cewa baya ga mutum duba goma da su ka rasa aiyukan su, ya ce su kan su masu masana’antun sun yi asarar fiye da naira biliyan ɗaya duk a dalilin annobar cutar korona.

A ƙarshe shugaban ya ce suna iyakacin ƙokarinsu wajen farfadowa daga wannan matsala da su ka faɗa tare da ganin sun dawo da ma’aikatan da su ka rasa aiyukan su bakin aiki, sai dai hakan nasu ya gaza cimma ruwa sakamakon mafi yawan ma’aikatan sun yanke ƙauna daga aiyukan tare da fuskantar da rayuwa a wasu ɓangarorin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *