Halin Da Mata Suke Ciki A Yau

Halin da mata suke ciki a yau!!
Sabuwar Jahiliyya…

Na dade ina kallon irin matsalolin da mata suka jefa kan su a ciki a yau…

Kaso mafi tsoka na ‘yan matan yanzu bokaye suke bi, sabuwar jahiliyya ta dawo. Tun kafin su shiga gidan mijin su suke kokarin rike masa wuya.

Idan kana neman karin aure to wadda zaka karo a matsayin ta biyu zatayi ta kokarin yadda zata fitar da wadda ta samu a ciki.

Ita ma ta ciki zata yi ta kokarin ganin waccan bata shigo ba sai wadda tsafin ta yafi karfi daga bokayen su.

Hatta da sabon gida idan mijin su ya gina kafin a tare Zaka ga kawaye suna zuwa suna bada shawarar kada su shiga haka nan su tafi wajen boka ya asirce mijin domin gidan ya zama nata ita kadai.

Ko yaya kaje wajen yarinya ta ganka da haske sai ta garzaya wajen boka a rike mata kai..wannan dabi’ar ta zama ruwan dare a cikin yan mata a wannan zamani. Ta kai har idan yarinya bata da boka to kawayen ta kallon ‘yar kauye suke mata.

Manyan shaidanun kuma sune kafiran mazaje bokaye da sune suke jefa su cikin wannan halakar.

Akwai asirin da ‘yan mata suke hadawa da gashin gaban su da jinin jikin su, su dafawa saurayi abinci mai rai da lafiya shi kuma kwadayayye ya zauna ya lashe tsaf.

Wata kuma da ruwan tsarkin da tayi ake hadawa ayi masa Zobo ko Ginger mai sanyi ya kur6e.

Wasu ‘yan matan kuma bokan zai sanya su a samo kwado a farde cikin sa a kwashe kayan cikin kuma a sake shi yaci gaba da tafiya yana tsalle….wannan shine shaidar asiri ya yi yadda ake so.

Akwai nau’ikan tsafi masu yawan gaske da ake amfani da su don mallaka ko cutarwa kawai saboda wani abu kalilan da zaa barshi a duniya.

Yawancin mutane a zamanin nan zaka gansu a rigar musulunci amma mushirikai ne, sun 6ata sun 6atar. Galibin wadanda aka fi halakarwa ta wannan hanyar sune mata, sai kuma maza da suma sun fara yawa a cikin wannan lamari.

Wannan masifar ita kadai ta isa Allah yayi ta aiko mana da musibu iri iri.

Mafita a gurin ka shine ka dimanci zikiran da suka tabbata daga Annabi S.A.W. kuma idan zaka yi aure kayi iya kokarin ka wajen nemo yar gidan tarbiyya..uwa uba shine bin Allah da manzon sa S.W.A

Allah ka shirya mu ka kiyashe mu 6ata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *