Almajiri Support Initiative: Shin Ko Kun Taba Cin Karo Labarin Abdul?

Usman Abdul ya kasance dan shekaru biyar (5) ne a Duniya sannan iyayensa sun tura shi Almajiranci. Ya kasance sai ya ta yawo a bisa kan titi yana bara kafin ya samu abinda zai ci. Idan Abdul bai da lafiya ya kan sadaukar da rayuwarsa ga Ubangijin da ya halirce sa don ba ya da kudin zuwa asibiti domin samun kulawan da ya kamata.

Yanzu shekarar Abdul 14 a Duniya ba karatun boko ko kuma takamammen sana’ar hannu domin dogaro da kai, rashin samun wadannan abubuwa a rayuwar sa ya sa Abdul ya kasance zai yi saukin yaudara.

Ba tare da samun wani matsala ba kungiyoyin ta’addanci daban-daban dake neman kananan yara domin su saka su Kungiyarsu don amfani da su wajen gudanar da ayyukar ta’addancinsu za su samu sauki wajen yin hakan; kungiyoyin ta’addanci suna ganin kananan yara kamar Abdul a matsayin makamai gudanar da ayyukansu. Wannan shine labarin Abdul da sauran yara almajirai kimanin miliyan 9.5 (kamar yadda binciken hukumar UNICEF na shekarar 2014 ta bayyana) Almajirai dalibai suna nan a baje a duk fadin Najeriya inda mafi yawancinsu sun kasance a Arewacin Najeriya.

Gidauniyyar Marasa Galihu ta Biya Farms Initiative For The Less Privilege ta lashe takobin dauke Kananan yaran nan daga bakin titi ta hanyar samar masu abinci, da kula da lafiyarsu tare da horas da sana’o’i da dama domin dogaro da kai. “Amma fa ba zamu iya yin hakan mu kai ba, shi ya sa mu ke bukatar tallafi daga al’umma domin samarwa almajirai gobe na gari.” – Gidauniyyar Biyar Farms ta ce.

Ku tallafawa gidauniyyar Biya Farms wajen samarwa yara kamar su Abdul gobe na gari. Za ku iya tallafawa ta hanyar danna NAN

Ku Kalli Bidiyon Shirin Gidauniyyar A Kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *