Sojojin Saman Najeriya Sun Kashe Mayakan Boko Haram Da Dama

Hedkwatar tsaro ta ce dakarun sojin saman Operation Lafiya Dole ta samu babban nasara ta hanyar halaka tushe da maboyar ‘yan ta’adda a yankin arewa maso gabas a ranar bikin zagayowar cikar Najeriya shekaru 60 da samun ‘yancin kai.

Shugaban fannin yada labarai na rundunar, John Enenche, ya sanar da hakan a wata takarda da ya fitar ranar Asabar a Abuja.

Manjo Janar Enenche, ya ce a ranar 1 ga watan Oktoba, dakarun sojin sun kashe ‘yan ta’adda masu tarin yawa a maboyarsu a Maima da Tusuy kusa da Warshale da Tongule a yankin Dikwa-Rann da ke Borno.

Ya ce nasarar an sameta ne bayan bayanan sirri da suka samu wanda ya bayyana inda ‘yan ta’addan suke kuma suke samun mafaka. Kamar yadda yace, dakarun sojin saman sun yi amfani da jiragen yaki masu dauke da bindigogi inda aka ragargaza wuraren buyarsu biyu.

A wani labari na daban, samamen da dakarun sojin sama na rundunar Operation Lafiya Dole karkashin Operation Hail Storm 2 suka aiwatar suke aiwatar ya cigaba da bada sakamako mai kyau.

Na karshen da ya faru shine ragargaza sansanin mayakan ta’addanci da kuma halaka wasu daga cikin ‘yan Boko Haram da ke Tongule, Bone da Isari B Musa a ranar 24 ga watan Satumban 2020.

Samamen da dakarun suka kai Tongule an kai shi ne sakamakon tabbacin da suka samu na cewa ‘yan ta’addan na zama a yankin da dare kadai. Kamar yadda ya yace, jiragen rundunar sojin saman dauke da bindigogin yaki sun kai hari yankin da dare, inda suka halaka da yawa daga cikin ‘yan ta’addan.

A Bone, kusa da yankin Yale-Kumshe, jiragen yakin sun kai samamen bayan tabbataccen bayanin sirri da suka samu. Jiragen dakarun sojin saman sun sakarwa yankin bama-bama tare da zuba musu ruwan wuta, lamarin da yasa sansanin da wasu mayakan suka halaka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *