Mun Haramtawa SARS Bincikar Ababen Hawa Da Wayoyi – Shugaban ‘Yan Sanda

Shugaban rundunar ‘yan sandan Najeriya ya haramtawa rundunar FSARS, STS da IRT binciken ababen hawa, kafa shingayen hanya da duba wayoyin yan najeriya. Hukumar yan sanda ne ta wallafa wannan sanarwan a shafinta na twitter.

Sanaewar ta kuma haramtawa duk wani jami’inta fita aiki da kayan gida ba tare da sanya kaki ko kuma wani sutura da hukumar ta tanada ba. Sannan sanarwar tace an kama wasu jami’an SARS da ake zargi da cin zarafin yan najeriya.

Ko a jiya jaridar Muryar Yanci ta kawo maku ruhoton yadda tsohon mataimakin shugaban kasa Alh Atiku Abubakar ya koka kan yadda jami’an rundunar SARS ke cin zarafin yan najeriya. Atiku ya koka ne musamman ganin yadda wani faifan bidiyo ya zagaye kafafen sada zumunta na zamani inda aka ga jami’an SARS suna cin zarafin wasu yan najeriya, lamarin da ya janyo ce-cekuce musamman a ciki da wajen Najeriya.

Daga karshe sanarwar da tafito daga ofishin sufeto janar tace duk wani jami’in da aka kama da karya wannan sabuwar doka, doka zatayi aiki akan kwamishinan yan sandan yankin da al’amarin ya faru.

Yan najeriya da dama sunji dadin wannan al’amari amman sunyi kira na musamman ga shugaba Buhari akan ya fito a talbijin ya bayyana wannan dokar ga yan najeriya domin ta hakan ne kawai jami’an tsaron da talakawa zasu kara tabbatar da aiki da dokar.

Ya kuke kallon wannan mataki da aka dauka akan jami’an SARS?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *